Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wace Irin Rawa Matasa Za Su Iya Takawa a Siyasar Najeriya?


Yayin da jam’iyyu ke kammala fidda 'yan takara domin fuskantar zabukan dake tafe a Najeriya, yanzu haka Matasa da kuma mata sun yunkuro domin damawa da su a zabe, musamman ta wajen tsayawa takara.

Ba tun yau ba ne dai kungiyoyin matasa da kuma na mata ke fafutukar ganin cewa su ma an dama da su a jagorancin kasa, musamman a matakin jihohi, batun da ya kai ga kafa wasu jam’iyyu da ke da taken matasa da ci gaba, ko da yake a wasu jihohin da sauran rina a kaba.

Amma kuma ba kamar wasu jihohi ba, domin a jihar Taraba Arewa maso gabashin Najeriya, lamarin ya soma sauyawa, inda matasa da dama suka fito takara ciki har da na kujerar gwamna.

Engr. Isa Musa Kantudu na jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP), ya ce wannan karon sai sun ga abun da ya turewa buzu nadi a wannan fafutuka.

A kullum, akan yi zargin cewa matasa su ne kan gaba, wajen tashe-tashen hankula. Amma sukan fito su musanta wannan ikrarin a ko da yaushe.

Kawo yanzu, tuni har mata a jihar Taraba suka rungumi gafaka don ganin ba'a bar su a baya ba a wannan karon.

Kamar yadda bincike ke nunawa, makudan kudade da kuma dauki-dora da suka gudana a wasu manyan jam’iyyu a Najeriya su suka tsorata wasu 'yan takara sauya sheka zuwa wasu sabbin jam’iyyu, musamman a wannan lokaci da ake ikirarin bai wa matasa damar shiga zabe.

Kwamared Abubakar AbdulSalam wani mai sharhi da fashin baki a Najeriya, na ganin muddin ba ayi gyara ba, siyasar kasar ka iya komawa hannun wasu mutane kalilan, wanda hakan kuma ba zai kai siyasar kasar ga gaci ba.

Bisa alkaluman hukumar zabe INEC, yanzu haka ana da adadin jam’iyyu kusan 91, ko da yake wasunsu ko ofisoshinsu ba’a sani ba, amma kuma suna da 'yan takara.

Amma wasu masu kula da al'umuran siyasa, sun nuna cewa, wasu daga cikin kananan jam'iyyun suna da manufofi masu inganci, duk da cewa 'yan takararsu ba su yi fice ba.

Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz kan irin rawar da matasa za su iya takawa a siyasar Najeriya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG