Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Kwararru Ke Cewa Kan Yadda Za A Inganta Tsarin Almajiranci A Najeriya


Wani lokaci da Kungiyar NOVAD ta tallafawa almajirai
Wani lokaci da Kungiyar NOVAD ta tallafawa almajirai

A Najeriya masana na ci gaba da tattaunawa akan sahihan hanyoyin da suke ganin su kadai za su iya share fagen inganta sha'anin almajiranci ga gwamnatocin da suka baiwa almajirai mazauni a jihohinsu.

Fiye da shekara daya kenan da gwamnatoci a Najeriya suka daura damarar dakatar da almajiranci a jihohin su inda wasu jihohin irin Kaduna da Kano suka fara tura keyar almajirai jihohin su na asali wasu kuma suka soma shirin inganta tsarin maimakon korar almajirai.

Tun a wannan lokacin ne jihar Sakkwato wadda ke arewa Maso yammacin Najeriya take tsare-tsare na kwaikwayon tsarin almajiranci na kasar Indonesia don inganta tsarin a jihar.

Sai dai akwai tsare-tsare da dole sai an yi aiki da su kafin haka ta cimma ruwa a wannan shirin, abinda ya sa masana suka hadu suka tattauna akan tsare-tsaren.

Dokta Bala Muhammad na Jami'ar Bayero ta Kano na ganin cewa tamkar tsarin karatun boko, shi ma wannan tsarin dole sai an samar masa manhajar karatu a cewar Farfesa Muhammad Ibn Junaidu.

Masu kula da wannan tsarin dai sun kwashe sama da shekara daya suna fadakar da jama'a amfanin sa.

To ko me yasa ake son amfani da tsarin na kasar Indonesia? Muhammad Lawal Maidoki wanda yana cikin ayarin gwamnatin jihar da suka ziyarci kasar ta Indonesia don nazarin kwaikwayon tsarin na su ya bayyana cewa tsari ne mai mahimmanci na tarbiya ga dalibi wanda ya amfani kasar ta Indonesia da ya sa duk da yawan su muka yawanci musuilmai amma ba sa yawon bara.

Masu lura da al'amurra dai na nuna fargaban dorewar wannan shirin a gaba, koda ya samu nasara a matakin farko, saboda muddin ba dukan jihohi suka hadu wuri daya ga aiwatar dashi ba akwai yuwar kwarorwar almajirai daga wasu jihohi zuwa inda ake aiwatar da shirin abinda kan iya kawo nauyin gudanar dashi ga jihar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG