Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Mamaki Ya Faru Sa'oi Kadan Bayan Fashewar Bam A Somalia


A Somalia wani abun ban mamaki ya faru sa’o’i kadan bayan wani mummunan harin bam da ya auku, wanda ya kashe mutane 358 tare da raunata daruruwan wasu mutanen a birnin Mogadishu ranar 14 ga watan Oktoba.

Daruruwan mutane sun garzaya asibitoci don bada gudunmuwar jini wannan wani abu ne da aka saba gani a kasashen yammacin duniya bayan aukuwar wani bala’i, kamar mahaukaciyar guguwar tekun da ta fatattaki birnin Houston dake nan Amurka kwanan nan.

Amma a Somaliya, kasar da kusan kullum tana cikin rikici, da nuna kyama, da tsoron allura ko samun karancin jini, na cikin abubuwan da suke hana yawancin mutane bada gudunmuwar jini.

A sakamakon haka, kasar ba ta da isassun wuraren adana jini fiye da shekaru 20 kenan yanzu, kuma nauyin bukatar yiwa mabukata karin jini ya dabaibaye asibitocin kasar.

Amma wani namijin kokarin canza wadannan dabi’un da wata kungiyar likitoci matasa suka yi ya taimaka a lokacin da aka kai harin ta’addanci na baya-baya nan a kasar.

Sai dai an maida wasu masu so su bada gudunmuwar jinin dayawa gida saboda asibitocin basu da wurin adana jinin da ba sa bukata nan take. Amma matasan likitocin sun yi amfani da wannan damar wajen yiwa masu neman bada gudunmuwar rijistar, koda za a bukacesu nan gaba, likitocin suka yiwa wannan tsarin lakabi da “ma’adanar jinimn jeka-dawo”.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG