Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abinda Ya Faru A Burkina Faso Zai Haifar Da Zanga-zanga A Nijar


A jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin fafitika sun kudiri aniyar gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi 30 ga watan Janairu da nufin nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da al’amuran mulkin kasar.

Kungiyoyin sun bada misalin yadda mahukunta suka gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi jama’a sai dai wasu makusantan gwamnatin ta Nijar na kallon abin tamkar wani yunkurin kwatanta abubuwan da suka faru a kasashe makwafta.

Sakin ragamar gudanar da zanga-zanga na daga cikin bukatun da shugabanin kungiyoyin fararen hula suka gabatar yayin ganawarsu ta farkon watan nan da shugaban kasa Mohamed Bazoum.

Mafarin da kenan kungiyoyin suka kudiri aniyar fitowa tituna a ranar Lahadin dake tafe a wasu biranen kasar da nufin bayyana damuwarsu akan abubuwa na ba daidai ba da suka ce suna wakana.

Sai dai a cewar Tsayabou Lawan Salao na RODDHAD wata kungiyar farar hular dake goyon bayan gwamnati ba za a rasa wata ajandar boye ba bayan wannan zanga-zanga a bisa la’akari da abubuwan da suka wakana a baya bayan nan a kasashe makwafka.

Shekaru sama da uku kenan ake ce-ce-ku-ce game da rashin samun ‘yancin gudanar da zanga-zanga a Nijar inda hukumomi ke bayyana dalilan tsaro da na anobar COVID-19 a matsayin hujjojin hanawa kungiyoyin fararen hula shirya jerin gwano ko gangami da makamantansa.

Lamarin da ya sa aka yi ta safa da marwa a kotuna saboda yadda sau dari irin wannan haduwa ke rikidewa zuwa tarzoma, to amma bayan gabatarwa shugaban kasa Mohamed Bazoum damuwarsu akan matakin hana zanga zanga ya basu tabbacin kawo karshen wannan matsala muddin suka mutunta doka.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Abinda Ya Faru A Burkina Faso Zai Haifar Da Zanga-zanga A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00


XS
SM
MD
LG