Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwa Da Dama Suka Janyo Ma Arewa Matsaloli


Gwamna Gaidam na Jihar Yobe yana gaida daya daga cikin mutanen da suka ji rauni a wani hari kan kasuwar dabbobi ta Potiskum.
Gwamna Gaidam na Jihar Yobe yana gaida daya daga cikin mutanen da suka ji rauni a wani hari kan kasuwar dabbobi ta Potiskum.

Rashin tarbiyya, talauci da rashin aikin yi a tsakanin matasa, sune kan gaba cikin abubuwan da suka haddasa matsalolin da arewacin Najeriya ke fuskanta.

Masu ruwa da tsaki a Jihar Yobe, sun ce dalilai masu yawa suka haddasa irin fitintinu da sauran matsalolin da Jihar da kuma yankin arewacin Najeriya baki dayansa ya fada ciki.

A wurin wani taro na masu ruwa da tsaki wanda Muryar Amurka ta shirya a Damaturun Jihar Yobe, akasarin masu jawabai sun ce rashin tarbiyya daga gida, da talauci da kuma rashin ayyukan yi, sune suka jefa matasa cikin fitinar da yanzu ta addabi Yobe da sauran arewacin Najeriya.

Wata mai halartar taron ta ce rashin cusa ma yara akidar sanin matsayin iyaye da makwabta da al'umma, na daya daga cikin abubuwan da suka sanya matasanmu su na tashi babu tarbiyya.

Wani malami yace musamman rashin aikin yi, yana sa matasa su rungumi abubuwan da ba su da kyau, tunda ba su da wani zabin.

Yace babban abin yi shi ne tabbatar da bin doka da oda, daga sama har zuwa ga kasa kan talaka. Haka kuma an bayar da shawarar a tattauna da 'yan bindigar dake kawo rashin tsaro a yankin, tare da rokon 'yan Boko Haram da su dubi irin hali na rashin kwanciyar hankalin da suka jefa iyaye da 'yan'uwansu a ciki.

Ga rahoton Sa'adatu Mohammed daga Damaturu.

Taron Da VOA Ta Shirya Kan Tsaro A Jihar Yobe - 2:46
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG