Accessibility links

'Yan Sara-Suka Sun Mika Makamansu Ga Hukumomi A Neja

  • Garba Suleiman

Matasa su na zanga-zanga a Najeriya

Matasan unguwannin Limawa da Daji a Minna, sun yarda sun sasantam sun kuma mika makamansu, bayan gabar shekara da shekaru da suka yi da juna

Matasan unguwannin Limawa da Daji a garin Minna, hedkwatar Jihar Neja, sun ayyana kawo karshen gabar da suka yi shekara da shekaru su na yi da juna, suka kuma mika makamansu ga hukumomi a wurin wani bukin da aka yi laraba a Minna.

A can baya, babu wani daga unguwa guda da yake iya shiga unguwar dayan ba tare da an kai masa farmaki ko kuma an dauki ransa ba.

Kwamishinar 'yan sanda a Jihar neja, ta ce an yafewa matasan dukkan abubuwan da suka faru a baya, muddin dai zasu rungumi wannan sulhu da aka kulla.

Mutumin da uya shiga gaba wajen ganin an samu wannan sulhu, Alhaji Yakubu Sallau, shugaban karamar hukumar Chanchaga, yace wannan rana ce ta farin ciki a saboda a can baya, mata ba su iya zuwa unguwa a wadannan unguwanni biyu, haka ma yara ba su iya watayawa.

Sakataren gwamnatin Jihar Neja, yace za a taimakawa matasan su koma makaranta, wadanda ba zasu iya ba kuma za a koya musu sana'o'in da zasu iya dogara da kansu.

Shugaban matasan unguwar Limawa, Yusif "Danger" Umar, yace su kansu matasan sun fara jin dadin wannan sulhu domin har sun fara shiga unguwannin juna, abinda ba ya iya faruwa a da.

Shi kuma shugaban daya bangaren matasan na unguwar Daji, Abdullahi "Duna" Musa, yace da yardar Allah an kawo karshen wannan matsala ta fadace-fadace a tsakanin matasan unguwannin.

Mustapha Nasiru Batsari ya aiko da cikakken rahoto daga Minna.

XS
SM
MD
LG