Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama ‘Yan Boko Haram 42 A Lagos Da Ogun


Wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka capke
Wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka capke

Wani kakakin rundunar sojan Najeriya yace wasu daga cikin wadanda aka kama din sun furta cewa sun tsere ne daga farmakin soja a arewa maso gabas.

Hukumomin Najeriya sun ce sun kama wasu mutane 42 da ake kyautata zaton cewa ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ne a Lagos, da makwabciyarta jihar Ogun.

Wani kakakin rundunar sojojin Najeriya a Lagos, Kingsley Umoh, yace wasu daga cikin mutanen har sun amsa cewa su ‘ya’yan kungiyar ce ta Boko Haram, kuma sun gudu daga yankin arewa maso gabashin kasar ne a saboda farmakin da sojoji ke kaiwa kan kungiyar tasu a wannan yanki.

Farmakin da sojoji suka fara kaiwa a tsakiyar watan Mayu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma Jihar Borno, inda ‘yan Boko haram suka yi tunga, ya nakkasa kungiyar, amma kuma ya sa ‘ya;yanta sun warwatse, wasu kuma sun buya. Majiyoyin tsaro suka ce kungiyar tana iya fadada hare-harenta zuwa wasu sassa.

A yanzu dai dukkan hare-haren Boko Haram sun ta’allaka a yankin arewacin kasar ne, ba a taba samun ire-irensu a Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, ko kuma yankin Niger Delta inda ake da masana’antun man fetur na kasar ba.

Wasu hare-haren bama-bamai da aka kai ranar litinin a Kano, birni mafi girma a yankin arewacin Najeriya, sun kasha mutane akalla 15 a unguwar Sabon Gari, wadda akasarin mazaunanta ‘yan kasuwa ne ‘yan kabilar Igbo, kuma mabiya addinin Kirista, daga kudancin Najeriya. A can baya ma, kungiyar Boko Haram ta auna hari a kan wannan unguwa.
XS
SM
MD
LG