Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abun da yakamata shugabannin arewa su yi


Kayan hada bama-bamai da yan sanda suka capke daga kungiyar Boko Haram
Kayan hada bama-bamai da yan sanda suka capke daga kungiyar Boko Haram

Abun Da Yakamata Shugabannin Arewa Su Yi Game Da Boko Haram

Mai ba shugaban Nageriya shawara kan harkokin yankin Neja kuma shugaban kula da shirye-shiryen bada ahuwa Mr. Kuku yace idan har ana son a cimma sulhu da kungiyar Boko Haram to wajibi ne manyan yan siyasan arewa da sarakunan gargajiya da shugabannin addini da ma masu fada aji su shiga cikin tattaunawar da za’a yi da kungiyar.

Mr. Kuku wanda yake jawabi a cibiyar Woodrow Wilson a birnin Washington DC ya fada ma wadanda suka halarci taron kara ma juna ilimi cewa tun da shugaba Jonathan ya kafa kwamitin neman daidaitawa da yan Boko Haram da kuma yi masu ahuwa to ya nuna ma duniya cewa hakika yana son zaman lafiya da tsaron kasar gaba daya.

Amma ya yi kashedi cewa idan manyan shugabannin arewa basu sa baki a tattaunawar ba to lamarin zai zama tamkar aikin banza harara a duhu. Shugaba Jonathan ya nuna adalci da gaskiya da kuma dagewa kan neman sulhu domin haka dole manyan arewa su taimaka a shawo kawunan shugabannin kungiyar Boko Haram. Yace shugabannin arewa sun san wadanda ke ma kungiyar jagoranata. Don haka yakamata su taimaka. Ta yin haka ne kadai haka zai cimma ruwa.

Ya yaba ma wadanda suka amsa zaben da aka yi masu na shiga kwamitin sulhun. Ya kwatanta yin hakan da aikin taimakon kasa. Yace ya amincewa abun da aka kirasu su yi ba maisauki ba ne to amma ya zama wajibi a yi domin kasar ta cigaba cikin kwanciyar hankali da lumana.

A yankin Neja Delta an cima daidaituwa ne bayan shugaba Yar’Adua ya nemesu da tattaunawa wanda ya dauki watanni da yawa ana yi kafin a kai ga yin ahuwa. A lokacin shugaba Jonathan shi ne mataimakin shugaban kasa shi ne kuma ya jagoranci tattaunawar tare da wasu masu fada aji daga yankin.
XS
SM
MD
LG