Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Alhazan Najeriya da Suka Rasu a Turmutsitsin Mina Ya Karu


Wasu alhazi sun kewaye wadanda aka tattakesu lokacin turmutsitsin 24 ga watan Satumba

An tabbatar da mutuwar alhazan Najeriya 199 a turmutsitsin ranar 24 ga watan Satumba a Mina kasar Saudiya.

Alkaluman da aka bayar yanzu sun nuna karin mutuwar alhazai 54 bisa ga adadin da aka bayyana tun can farko.

Kwamishanan labarun hukumar alhazan Najeriya Shaikh Sale Okenwa ya sanarda hakan a wani karin bayanai da ya bayar.

Har yanzu ana neman alhazan Najeriya 111 da kawo yanzu ba'a san inda suke ba ko suna da rai ko kuma sun rasu. Akwai mutane biyar da ake jinyarsu.

An yi taron addu'ar bankwana ga alhazan da suka fito daga kasashen Afirka inda jihar Kebi ta samu ta ciyar da wasu alhazan. Kanar Samaila Yombe Dabai mataimakin gwamnan jihar Kebbi ya yiwa alhazan da suka rasu addu'a.

Sarkin Argungu ya yi korafi kan wurin da ake ajiye alhazan Najeriya wanda yake da tazarar kilomita biyar daga wurin jifar Shaidan. Yace an yi kusan shekaru 20 ana ajiye 'yan Najeriya a wurin. Ya kamata a canza masu. Sun kuma mika korafin ga mahukuntar kasar ta Saudiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG