Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kawo Yanzu Turmutsitsin Saudiya Ya Hallaka Alhazan Najeriya 56


Sakamakon turmutsitsin da ya auku ranar Alhamis a Saudiya
Sakamakon turmutsitsin da ya auku ranar Alhamis a Saudiya

Kimanin mutane 717 suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin da ya faru ranar Alhamis a Saudiya cikinsu mutane 56 da aka tabbatar 'yan Najeriya ne.

Shugaban hukumar alhazan Najeriya Barrister Abdullahi Mukhtar Muhammad ya bayyana adadin alhazai 56 da suka rasa rayukansu a sakamakon turmutsitsin tafiya jifar Shaidan a Mina.

Alhazai 42 suka rasu daga jihohi. Biyu daga hukumar alhazai ta kasa sai kuma goma sha biyu daga kamfanonin jiragen yawo.

Shugaban hukumar yace an kafa kwamitoci karin bincike, ta'aziya da shirin jana'izar marigayin.

Jakadojin Najeriya dake Riyadh da Jidda sun kasance a wurin bisa ga umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari saboda su yi aki tare da kuma karfafa masu gwiwa.

Har wa yau akwai gawarwakin da kawo yanzu ba'a tantancesu ba. Likitan alhazai Dr Ibrahim Kana yace za'a yi anfani da dabarun likita wajen ganosu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG