A yau Laraba, jami'an kiwon lafiya na kasar China, sun ba da rahoton cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar Coronavirus, ya haura 1,100.
Hukumar kula da Lafiya ta kasar ta kara adadin mace-macen da aka samu zuwa 97 bayan haka an tabbatar da cewa mutane 44,653 sun kamu da cutar, tun bayan barkewar ta a watan da ya gabata. Ko da yake wasu masana sun nuna shakku game da yawan adadin mace-macen.
Gungun mutane mafi yawa da suka kamu da cutar su ne wadanda ke cikin wani jirgin ruwa a Yokohama da ke kasar Japan, inda mutane 174 daga cikin mutane 3,700 da ke cikin jirgin suka nuna alamun kamuwa da cutar, yayin da har yanzu ake tsare da jirgin.
Kasar China ta dakatar da harkoki a wasu sassan kasar, a kokarin dakile yaduwar kwayar cutar.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 21, 2023
Saudiyya Ta Ce Ranar Alhamis Watan Azumi Zai Kama
-
Maris 17, 2023
Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin
-
Maris 13, 2023
Shugaba Buhari Ya Taya Xi Jinping Murnar Sake Lashe Zabe
Facebook Forum