Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Coronavirus a Najeriya Ya Doshi 6000


A cikin sabbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar coronavirus.

A cewar NCDC, mutum 338 ne cutar ta sake harba, wanda hakan ya mayar da adadin masu cutar zuwa 5,959 a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabin mutum 177. Sai jihar Kano wacce ke biye da ita da Karin mutane 64, Sai kuma birnin tarayya Abuja dake da karin mutane 21.

Sauran jihohin sun hada Rivers 16, Plateau 14, Oyo 11, Katsina 9, Jigawa 4, Kaduna 4, Abia 3, Bauchi 3, Borno 3, sai jiohohin Gombe, Akwa Ibom, da Delta na da guda biyu-biyu, jihohin Ondo, Kebbi, da Sokoto na da guda daya-daya.

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutane 5,959 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 1,594 suka sami lafiya, sai kuma mutane 182 da suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG