Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 Ya Haura 120,600 a Najeriya


Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ya kai 1,633 a ranar Asabar kadai a Najeriya a cewar hukumar NCDC mai sa ido akan cututtuka masu yaduwa.

Yanzu gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya ya kai 120,602 ya zuwa daren Asabar, 23 ga watan Janairu, a cewar hukumar ta NCDC.

A bayanan da ta ke fiddawa a kowacce rana a shafinta na Twitter, NCDC ta ce an samu karin mutum 1,633 da suka kamu da cutar a ranar Asabar.

Hukumar ta kuma ce cikin mutum 120,602 da suka kamu da cutar mutun 95,901 sun warke kuma an sallame su daga asibiti yayin da mutum 1,502 suka mutu.

Hukumar ta kuma sanar da cewa an samu karin adadin ne daga jihohi 21, ciki har da jihar Legas, inda aka samu karin mutum 498 sai kuma jihar Filato da ke biye da mutum 214.

Sauran jihohin sun hada da birnin tarayya Abuja mai mutun-176, Rivers-99, Kaduna-98, Edo-87, Anambra-86, Akwa Ibom-50, Osun-47, Kano-40, Oyo-40, Kwara-39, Ebonyi-28, Niger-28, Taraba-28, Ogun-27, Ondo-21, Ekiti-12, Katsina-7, Borno-6, sai kuma Delta-2.

XS
SM
MD
LG