Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Mutu a Ayarin Gwamna Zulum Ya Kai 30 - AFP


Gwamna Zulum, tsakiya sanye da malafa, yayin ziyarar da ya kai garin Baga (Hoto: Twitter @ProfZulum)
Gwamna Zulum, tsakiya sanye da malafa, yayin ziyarar da ya kai garin Baga (Hoto: Twitter @ProfZulum)

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito cewa adadin mutanen da suka mutu a harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan ayarin motocin gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya kai 30.

Wasu majiyoyi biyu sun fadawa AFP cewa, an gano karin wasu gawarwaki bayan harin wanda aka kai a ranar Juma’a .

Karin wadanda aka gano, sun hada da ‘yan sanda 12, sojoji biyar, da wasu ‘yan sintiri na civilian JTF hudu da kuma fararen hula tara a cewar kamfanin dillancin labaran.

Gabanin gano karin wadanda suka mutun, majiyoyin sun fadawa AFP cewa, wasu mahara sun afkawa ayarin gwamnan jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum a yankin garin Baga da ke kusa da yankin Tafkin Chadi.

Ko a watan Yulin da ya gabata, ayarin motocin gwamnan ya fada tarkon maharan a kusa da garin na Baga, lamarin da ya tilasta masa janye ziyarar da ya yi shirin kai wa a lokacin.

Mayakan ‘yan ta’adda na ISWAP ta yammacin Afirka da ke da alaka da kungiyar IS, sun dasa matsugunansu a tsibiran da ke yankin Tafkin Chadi – yankin da ya zama masu tunga.

A baya-bayan nan kungiyar ta zafafa hare-haren da take kai wa akan dakaru da fararen hula a yankin.

Rikicin Boko Haram, wanda aka kwashe sama da shekara goma ana yi a arewa maso gabashin Najeriya ya halaka mutum dubu 36 kana ya tilastawa sama da mutum miliyan biyu ficewa daga muhallansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG