Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Gobara ta lakume babbar kasuwar Yola


Adamawa: Gobara a babbar kasuwar Yola

Gobarar babbar kasuwar Yola tayi sanadiyar hasarar dukiyoyin miliyoyin nera

Gobarar da ta tashi wajejen karfe uku na safiyar yau ta kone fiye da kashi casa'in na kasuwar.

Mutane da jami'an kwanakwana sun yi kokarin kashe wutar amma ta cigaba da ci saboda matsalar hanyar shiga kasuwar da motocin kwanakwana.

Rahotanni sun nuna gobarar ta tashi ne cikin dare sakamakon matsalar wutar lantarki.

Shugaban 'yan kasuwar Ali Kachalla yace wutar ta fara ne da misalin karfe uku kuma da ya shiga kasuwar shawo kan wutar ya fi karfinsu. Shi ma yace tabbas matsalar wutar lantarki ce ta jawo gobarar

Shi ma shugaban 'yan kasuwar jihar Alhaji Ibrahim Muhammad 86 yace su 'yan kasuwar jihar Adamawa sun tashi da bakin ciki. Wutar ta kwashi wajen sa'o'i hudu tana ci. Har yanzu ba su iya kiyasta adadin hasarar da suka yi ba.

Tawagar gwamnatin jihar ta ziyarci kasuwar inda kwamishanan kasuwanci da masana'antu na jihar ya yi bayani cewa gobarar babbar hasara ce ga jihar kuma zasu duba su ga abun da gwamnatin jihar zata iya yi.

Kwamishanan yada labarai na jihar Ahmed Sajoh yace gobarar zata kara matsalar abinci domin yankin da ake sayar da hatsi a kasuwar ya kone.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Adamawa Yola Gobara
Adamawa Yola Gobara

XS
SM
MD
LG