Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Tofa Albarkacin Bakinta Kan Hare-Haren Kunar Bakin-Wake


Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Rabe Abubakar, yace ko da an murkushe akjasarin 'yan ta'adda, gano masu aikata kunar-bakin-wake yana da matukar wuya

Yayin da ake ganin alamun samun galaba a kan 'yan ta'adda na kungiyar Boko Haram a Najeriya, an ci gaba da fuskantar hare-haren kunar-bakin-wake a wasu jihohin kasar, musamman ma a yankin arewa maso gabas.

A cikin kwanaki biyun da suka shige, an samu hare-haren kunar-bakin-wake a jihohin Borno da Adamawa, inda mutane masu yawa suka rasa rayukansu.

Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Rabe Abubakar, yace koda a kasashen da suke da karfin soja fiye da Najeriya, a kan ga irin wadannan hare-haren kunar-bakin-wake wadanda ;'yan ta'adda ke amfani da su a bayan an murkushe su an hana su sakat.

Yace gano su yana da matukar wuya tunda ba wai wani kaya ne dabam suke sanya a jikinsu ba, "su na amfani da yara kanana da 'yan mata su na kashe kawunansu wajen kai hare-hare."

Birgediya Janar Abubakar ya ce su na daukar matakan ganin sun kawo karshen irin wadannan hare-haren tare da samun nasara.

Wani tsohon hafsan mayakan saman Najeriya, Aliko el-Rashid Harun, wanda ya kware a fannin ayyukan tsaro, yace kamar yadda ake gani a duk inda irin wannan ta'addanci ke faruwa a duniya, misali a Syria da Iraqi da wasu wuraren, nauyin kawo karshen ta'addanci ba a wuyan gwamnati kadai yake ba.

Yayi misali da cewa mutane da dama sun san akwai sansanonin 'yan Boko Haram a tsakanin Dumbulwa da Zango dake Jihar Yobe da wuraren Nafada da Ashaka a jihar Gombe, amma kuma su na tsoron yin magana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG