Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ado Ahmed Gidan Dabino ya Sami Lambar Girma ta MON.


Ado Ahmed Gidan Dabino Lambar Girma
Ado Ahmed Gidan Dabino Lambar Girma

A cigaban matasa wani matashi mai suna Ado Ahmed Gidan Dabino wanda yasami lambar girma ta (MON) a matsayin mai yiwa kasa hidima ta hanyar cigaban harshen Hausa, Ado Ahmed dai yasami wannan lambar girman inda shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika masa wannan lambar.

Matashin dai ya bayyana jin dadinsa game da samun wanna kyauta ya kuma yi kira ga matasa, inda yace, “a kiran dazanyi shine duk wanda ya shiga kowace irin sana’a ko harka ko aiki da a yishi tsakani da Allah yayi gaskiya, mutum yazama budadde kada yaji tsoro, sannan kada kasa abu aranka ko da kudi ko babu karkace kudi sune komai a rayuwa.”

Ado Ahmed dai yaja kunnen matasa dasu kauracewa kudin gaggawa muddin suna son cigaban al’ummarsu da rike mutuncinsu domin da mutunci zaka iya samawa kanka suna nagari, har 'ya'yanka su mora koda kuwa bayan ranka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG