Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan: Ghani Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Gillar Da ISIS Ke Yi


Wasu 'yan kungiyar ISIS suna shirin fillin kawunan wasu mutane da suke garkuwa da su
Wasu 'yan kungiyar ISIS suna shirin fillin kawunan wasu mutane da suke garkuwa da su

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya yi Allah-wadai da fille kawunan wasu farar hula da Kungiyar ISIS ta yi a kudancin kasar, inda nan ne ma kwanan nan aka fafata tsakanin bangarorin kungiyar Taliban.

Shugaba Ghani ya fadi a wani jawabi yau Litini cewa ya na mai yin tir da datse kawunan farar hula, musamman ma mata da yara.

'Yan sandan lardin Zubar sun ba da rahoto jiya Lahadi cewa mayakan ISIS sun yi kisan rashin imani ma mutane 7, ciki har da mata 3, a gundumar Khake-e-Afghan.

Ya kara da cewa yana ganin wannan danyan aikin wata alamace ta takura da kuma gazawar makiya mutanen Afghanistan.

Jami'an Afghanistan sun ce mayakan ISIS sun kama mutanen, wadanda 'yan kabilar Hazara ne 'yan mazhabar Shi'a, sama da wata guda da ya gabata a lardin Ghazni da ke kusa da wurin.

Shugaban ya fadi a jawabin nasa cewa zai kira taro na musamman kan batun tsaro a yau dinnan Litini don duba yadda za a farauto tare da ladabtar da wadanda su ka aikata wannan danyan aikin.

Kungiyar ISIS, wace ke iko da wurare masu yawa a Iraki da Siriya, sannu a hankali ta na wanzuwa a Afghanistan kuma ta kafa tungaye masu karfi a gundumomi da dama da lardin Nangarhar da ke gabas, wanda ke iyaka da Pakistan.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG