Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan: Kungiyar Taliban Ta Bada Sanarwar Fara Kai Munanan Hare-hare


Mayakan Taliban

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da zabuka a Afghanistan kungiyar Taliban ta sanar da fara kai munanan hare-hare da zasu dakile shirin komawa kan taeburin tattaunawa


Kungiyar Taliban ta bada sanarwar fara kai munanan hare harenta na shekara a Afghanistan, wanda zai haifar da koma baya ga shirin makwanni da aka yi na sake komawa ga teburin tattaunawa. Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Aghanistan ke shirin gudanar da zaben wakilan majalisar dokoki da na kananan hukumomi a cikin watan Oktoba, wanda ka adade ana samun jinkiri gudanarwa.


Wannan ayyukan yan ta’adda da aka mai take Al Khandag, ya fara ne da safiyar jiya Laraba kuma wadannan hare hare zasu fi auna Amurkawa da yan leken asirinsu da suka mamaye kasar a cewar sanarwar Taliban.


Wannan mataki ya zo ne yan makwanni bayan da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya amince a wurin wani taron kasa da kasa a birnin Kabul ya tattauna da kungiyar Taliban ba tare da gitta wasu sharuda ba, domin kawo karshen fadar shekaru 17 da yaki ci yaki cinyewa.


A wata hira da yayi kuma aka yada a kan wani talbijin Pakistan mai zaman kansa da yammacin jiyar Laraba, jakadar Afghanistan a makwabciya Pakistan Omar Zakhilwal ya daga akan cewa Taliban bata da karfin da zata yi galaba a kan sojoji, a don haka ta bada hadin kai a koma ga tattaunawa domin kawo karshen mummunar yakin Afghanistan.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG