Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan: Mayakan Taliban Sun Kai Hari Kan Majalisar Dokoki


Ma'aikatan agaji suna taimakawa wadanda suka jikata a harin da mayakan Taliban suka kai kan majalisar dokoki
Ma'aikatan agaji suna taimakawa wadanda suka jikata a harin da mayakan Taliban suka kai kan majalisar dokoki

Mayakan Taliban dauke da muggan makamai sun kai hari kan majalisar dokokin Afghanistan a birnin Kabul, harin ya hada da kunar bakin wake, fashe fashe da kuma harbi da bindigogi a wajen ginin majalisar , yayinda wakilai suke ciki suna aiki.

An fara harin ne da wata gagarumar fashewa wani bom a babbar kofar shiga harabar majalisar. Wasu fashe fashe da suka biyo ba sun sa anga hayaki na tashi daga ginin, lamarin da ya sa hayakin ya turnuke har cikin ginin, yayinda 'yan majalisa suka tsere cikin tsoro.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar yace mayakan Taliban su bakwai wadanda suka yi damara da nakiyoyi suna daga cikin wadanda suka kai harin, kuma dukkansu jami'an tsaro sun kashe su, wanda ya kawo karshen kawanyar da aka yiwa majalisar na kusan sa'o'i biyu.

Ma'aiktar tace babu wakilin majalisa da ya jikkata sakamakon harin, amma jami'an kasar suka ce akalla wasu mutane 30 sun jikkata, cikinsu harda mata biyar da yara uku, wasu raunukan da suka samu suna da tsanani.

Ofishin jakadancin Amurka dake Kabul ya fidda sanarwa inda yayi Allah wadai da harin, yana cewa "kai hari kan majalisa ya nuna a fili rashin mutunta tsarin Demokuradiyya da doka da Oda"

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG