Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFGHANISTAN: Mutane Takwas Sun Rasu A Harin Da Aka Kaiwa Filin Wasa


Wani jami'in dan sanda yana gudanar da bincike a wurinda aka kai hari a filin wasan Kirket

Wadansu jerin fashe fashe sun kashe a kalla farin kaya takwas suka kuma raunata sama da arba’in a gabashin Afghanistan

Attaullah Khogyanai, kakakin larfin Nangarhar dake gabashi ya shaidawa Muryar Amurka cewa, fashe fashen sun auku ne a Jalalabad da dare a filin wasan kirket lokacin ana cikin wasa.

Khogyanai yace dukan fashe fashen uku sun auku ne a cikin filin wasan da misalin karfe goma sha daya da rabi na dare agogon kasar.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai Hedyatullah Zahir Kamawal, babban jami’in shirya gasar cin kofin na Ramadan, wani sabon rukunin gasa da aka shirya gudanarwa a lokacin azumin Ramadan.

Kawo yanzu hukumomi basu tabbatar da irin fashe fashen ba, sai dai sunce ‘yan sanda suna wurin suna gudanar da bincike.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin hare haren bom din, sai dai hukumomin suna zaton kungiyar IS ke da alhakin hare haren.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG