Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Yi Asarar Dala Biliyan 190 Sanadiyyar Annobar COVID-19


Shugaban bankin raya kasashen Afirka, Akinwumi Adesina. REUTERS/Amit Dave - RTX36ZWZ

A cewar Akinwumi, gabanin barkewar annobar, akwai kasashe 6 a nahiyar da tattalin arzikinsu ya hau turbar zama tattalin arzikin da ke bunkasa a duniya.

Bankin raya kasahen Afirka AFDB, ya ce nahiyar ta yi asarar tsakanin dala biliyan 145 zuwa dala biliyan 190 tun bayan barkewar annobar COVID-19.

Shugaban bankin Dr Akinwumi Adesina ne ya bayyana hakan a shafin bankin na Twitter.

“Irin tasirin da annobar ta yi akan tattalin nahiyar yana da giman gaske. Daukacin asarar kudaden shiga na cikin gida da nahiyar ta yi, ya kai tsakanin dala biliyan 145 zuwa 190.”

A cewar Akinwumi, gabanin barkewar annobar, akwai kasashe 6 a nahiyar da tattalin arzikinsu ya hau turbar zama tattalin arzikin da ke bunkasa a duniya.

“Amma an samu sauyi, bayan da aka rufe harkokin tattalin arzikin kasashe, kamar na tafiye-tafiye da fannin yawon bude ido duk sun kafe, yayin da farashin kayayyakin suka fadi.

“Afirka na bukatar hanyoyi da dama don farfado da tattalin arzikinta. Kasashen da ke kudu da hamadar Sahara wadanda ba su da kudaden shiga, za su bukaci dala biliyan 245 nan da shekarar 2030. Sannan daukacin kasashen yankin za su bukaci dala biliyan 425 nan da 2030.” In ji Adesina.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG