Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Okonjo-Iweala Ta Kai Ziyarar Farko Najeriya Bayan Zama Shugabar WTO


Shugabar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala

A karon farkon tun bayan da ta karbi ragamar tafiyar da hukumar kasuwanci ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta kai ziyara kasarta Najeriya.

Okonjo-Iweala ta isa kasar ne a ranar Asabar, don yin ziyarar aiki ta kwana hudu da zimmar ganin yadda za a bunkasa harkokin cinikayya da tattalin arzikin kasar.

Rahotanni daga Najeriyar sun ce yayin wannan ziyara, shugabar ta WTO za ta gana da shugaba Muhammadu Buhari don duba yadda za a farfado da ayyukan da za su bunkasa tattalin arzikin kasar.

Har ila yau ziyarar ta ta, ta hada da nuna godiya ga shugaban kasar kan irin goyon bayan da gwamnatinsa ta nuna mata wajen samun wannan mukami.

Sabuwar babbar daraktar hukumar kasuwanci ta duniya wato WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta fara aiki gadan-gadan a hukumar ne a ranar Litinin 1 ga watan Maris, Shekarar 2021.

A 'yan kwanakin nan ne Majalisar zartarwar hukumar kasuwancin ta duniya ta zabi Ngozi Okonjo-Iweala, bakar fata kuma ‘yar Nahiyar Afirka ta farko da ta taba rike mukamin tsohuwar ministar kudi ta Najeriya sau biyu a matasayin babban daraktar hukumar ta 7.

Bayan samun nasara da ta yi a matsayin babbar daraktar hukumar, Okonjo-Iweala ta bayyana tsare-tsaren ta da suka hada da yin aiki tare da sauran mambobin hukumar wajen sauya fasali da canja tsarin hukumar kasuwancin ta duniya.

A cewarta, kundin tsarin jagorancin hukumar kasuwancin da ke da mazauni a birnin Geneva, na bukatar gyara sakamakon yadda wasu manufofinta musamman yarjejeniyoyin kasa-da-kasa na wasu shiyoyi wanda su ke shigar da wasu kera-Keren zamani.

XS
SM
MD
LG