Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Layin Dogo: Wasu Masu Gonaki Na Neman A Biya Su Diyya A Kano


Wasu manoma suna aiki a gonarsu a Najeriya

Yayin da aikin gina sabon layin dogo wato jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano ya fara kankama, al’umomin da aikin zai ratsa ta gonakinsu, na ci gaba da korafin rashin biyan diyya, har ma suka bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya baki domin tabbatar da adalci a gare su. 

Ko da yake, a rangadin da ministan sufurin kasar Rotimi Ameachi ya kai kimanin makonni biyu baya domin ganin yadda aikin ya fara gudana, ya ce gwamnati ta kammala biyan kowa diyya, amma daga bisani al’umomin na ci gaba da bayyana rashin gamsuwa.

Dayyabu Umar na cikin daya daga cikin dubban manoma da aikin shimfida layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna ya ratsa da gonakin su, wadda gwamnatin Najeriya ta baiwa wani Kamfanin kasar China akan biliyoyin dala, ya kuma ce an bai wa mutum biyu hakki, wasu kuma ba a ba su ba, an ce kasa ta gwamnati ne, ba ta tallaka ba ce.

Sai dai Alhaji Sagir Sulaiman da ke zaman manajan shiyyar arewa maso yamma na kamfanin dake kula da kadarorin hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya ya ce akwai matakan da suka bi wajen biyar diyyar.

Amma wadannan al’umomin da wannan aikin hanyar jirgin kasa ya tafi da gonakinsu, sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya shiga cikin wannan lamari.

A watan Yulin bara, shugaba Buhari ya kaddamar da aikin layin dogon, wanda ya tashi daga Kano zuwa Kaduna, wanda har ila yau zai hade da layin dogo na Abuja.

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG