Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 37 Tashin Bamabamai Ya Kashe a Iraqi


Wani wurin da bam ya tarwatse daga cikin wata mota
Wani wurin da bam ya tarwatse daga cikin wata mota

A 'yan kwanakin nan kasar Iraqi na fama da fashewar bamabami kuma kowane fashewar rayuka da dama na salwanta

A Iraqi an kashe akalla mutane 37 a wasu jerin hare haren bama-bamai a fadin kasar jiya Litinin.

'Yansanda suka ce bam mafi girma ya tashi ne kusa da wata kasuwa cike makil da mutane a yankin da galibin mazauna garin da ake kira Khalis 'yan masahabar shi'a ne,har mutane 15 suka mutu. Garin yana da tazarar kilomita 80 daga Bagadaza.

Hari na biyu ya halaka mutane 10 a wata kasuwa a wurin da ake kira Al-Zubair, wanda yake arewa maso gabashin babban birnin kasar.

Yayinda a Bagadazan, 'Yansanda suka ce, wani bam da aka boye cikin mota ya tashi a gundumar Hussainiya dake hanyar fita birnin daga arewa, ya kashe mutane 12, kamar dai yadda ma'aikatan kiwon lafiya da 'yansanda suka bayar.

Duk da yake babu wanda ya dauki alhakin kai hare haren, kungiyar ISIS a baya ta dauki alhakin wasu hare haren data kai da niyyar wargaza gwamnatin kasar.

XS
SM
MD
LG