Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 12 Ne Suka Rasu a Kunar Bakin Waken Kano


Wani harin bam a Kano

Baya ga harin kunar bakin waken da aka kai a Fataskum yau, dazun nan ma ya faru a kano ya kashe akalla mutane 12

Yau din nan aka kai wani harin kunar bakin wake a jihar kanon Najeriya wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 12 amma biyu daga daga cikin su ana kyautata zaton wadanda suka kai harin ne.

Wakilin muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari yayi hira da wani mutum wanda ya je kai daukin gaggawa yace “yaji karar fashewar tagwayen bamabaman kuma ya ga wuta ta shi”. Wannan wurin da bam din ya tashi dai babban wuri ne da ake shiga mota zuwa wasu jahohin Najeriya.

Bayan ‘yan mintuna kadan da fashewar bam din kwamishinan ‘yan sandan jahar Kano Alhaji Ibrahim K Idris ya bayyana kuma kakakin rundunar ‘yansandan ASP Magaji Musa ya tabbatar da faruwar abin kuma yace suna ta kokarin ceton jama’a ne dan haka a wannan lokcin mutum 12 kawai ne suka rasu.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG