Jama’a Na Tserewa Hare-Haren Da Sojojin Saman Najeriya Ke Kaiwa ‘Yan Boko Haram – 25 Ga Fabrairun 2015
Rundunar sojojin Najeriya sun fidda wani majigin bidiyon da ke nuna yadda suke ratattakar ‘yan kugiyar boko haram da bama-bamai ta sama a arewa maso gabashin kasar da nufin cika kudurin murkushe ‘yan ta’addar. Bidiyon da muryar Amuryar ta samu daga tashar talbijin ta Channels ya nuna yadda mutanen yankin ke ta gudu a gigice a yankin da sojin ke ganin nan ne maboyar ‘yan kungiyar. Kakakin sojojin Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade yace an kai harin na sojojin sama a yankunan Gwoza da Bama da kuma dajin Sambisa cikin nasara.
Labarai masu alaka
Zangon shirye-shirye
-
Satumba 23, 2023
Yi Wa Shugabanni Addu’a Shi Ne Zai Hana Su Lalacewa - Gawuna
-
Agusta 03, 2023
Zanga-zangar Lumana Ta Kungiyar NLC a Abuja