Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutune 100 Suka Kamu Da Coronavirus a Jihar Tahoua, Nijer


Ya zuwa ranar Asabar 9 ga watan Janairu babban asibitin garin Galmi da ke jihar Tahoua a jamhuriyar Nijer ta yi rijistar mutane 100 da suka kamu da cutar coronavirus, ciki har da jami'an asibiti.

Mutane 100 ne suka kamu da cutar coronavirus a yankin, a cewar rahotanni daga assibitin Galmi da ke gundumar Malbaza a jihar Tahoua, Jamhuriyar Nijer.

Daga cikin wadanda suka kamu da cutar har da ma'aikatan kiwon lafiya na wannan asibitin kamar yadda daya daga cikin malaman asibitin na Galmi ya bayyana, ya ce cikin mutane 100 akwai ma'ikatan kiwon lafiya 30 da suka kamu da cutar.

Asibitin na Galmi na karbar marasa lafiya da suka fito daga ko'ina a jihar Tahoua da ma sauran jihohin Nijer da kasashe makwabta, musamman Tarayyar Najeriya da ta hada iyaka da wannan yankin.

Wani likita a asibitin na Galmi Mathieu Maygal, ya bayyana irin matakan da suke dauka domin dakile yaduwar annobar coronavirus ya kuma kara jaddada wasu daga cikin alamomin da ake gani na kamuwa da cutar da suka hada da ciwon kai, zawo, masassara, ciwon makogoro, rashin kamshi ko wari. Ya kara da nanata muhimmancin wanke hannu da sanya takunkumin rufe hanci da baki.

Taron majalisar ministocin da ya gabata ya dauki nauyin bude wurin killace wadanda suka kamu da wannan cutar a garin Malbaza da kuma kara wa asibitin Galmi kayan aiki na kula da masu cutar da ma tallafa wa malaman asibitin don kara basu kuzari bayan da wata tawaga daga ofishin ministan kiwon lafiya ta je Galmi don gane wa idonta halin da a ke ciki.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00

XS
SM
MD
LG