Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Alamar Wasu Kasashe Zasu Yi Katsalandan A Zaben Amurka


Shugaba Trump

Kasashen Rasha da China da kuma Iran suna nan suna shirya katsalanda a zaben shugaban kasar Amurka da zummar Amurkawa su zabi dan takarar da suke so ya shiga fadar White House, a cewar wani muhimmin kashedi da babban jami’in hukumar yaki da masu liken asiri a Washington.

Darektan cibiyar yaki da masu liken asiri da tsaro ta kasa, William Evanina ya ce ma’aikatar tattara bayanan sirrin Amurka ta fada cewa kasashen ukun sun dukufa wurin rarraba kawunan Amurka da kuma lalata harkokin demokararadiyar Amurkawa.

Amma ya ce Rasha da China da kuma Iran sun samu sabani a kan mutumin da suke so su ga ya lashe zaben shugaban kasa a cikin watan Nuwamba tsakanin shugaban Donald Trump da abokin karawar sa na Democrat, mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

Mun gano cewa Rasha tana daukar matakai da dama na zubarwa mataimakin shugaban kasa Joe Biden da mutunci da ma ma jami’iyar Democrat da take mata kallon abokiyar gabar Rasha, inji Evanina a wata sanarwa ta yammacin jiya Juma’a, inda ya ce yunkurin Moscow ya yi daidai da sukar da Kremlin ke yiwa Biden da tsohon shugaba Barack Obama.

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG