Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Kwarin Gwiwar Za'a Gano Jirgin Malaysia da Ya Bace


Marshal Angus Houston mutumin Australia dake zaton za'a gano jirgin
Dan kasar Australia mai shugabantar tawagar masu aikin neman jirgin saman kasar Malaysia da ya bata a karkashin tekun Indiya, ya na bayyana kwarin guiwar cewa za a iya gano jirgin nan kusa.

Angus Houston ya fada a jiya Laraba cewa sautuka biyun da wata na'urar jirgin mayakan ruwan Amurka ta jiyo shekaranjiya ya baiwa masu bincike dalilin kyautata fatar cewa za su gano mushen jirgin saman.

Yana cewa "Yanzu ina kyautata zaton cewa za mu samo jirgin saman cikin wani dan kankanin lokaci nan gaba."

Houston ya ce sautukan baya-bayan nan za su taimaka wajen takaita wurin da ake aikin neman jirgin saman a yammacin Australia, aikin ya zama a wani wuri mai saukin dubawa sosai, amma ya kara da cewa kafin su tabbatar da cewa a wurin jirgin saman ya fadi ana bukatar 'yan kasa da kasa masu aikin neman jirgin saman su ga mushen jirgin da idon su tukuna.

Ya ce ana bukatar jin karin sautuka kuma a kyautata yanayin wurin binciken kafin hukumomi su tura wani jirgin karkashin ruwa mai sarrafa kan shi ya binciki karkashin teku.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG