Accessibility links

Akwai Sojojin Najeriya a Boko Haram – inji Sojan Najeriya – Kashi na Hudu


Wani mutum da yace shi sojan Najariya ne daga Kwanduga a jihar Borno, ya fadi irin abubuwan dake wakana a bayan fage, dangane da yaki da kungiyar tayar da kayar baya da aka fi sani da Boko Haram, a hirar da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto na sashen Hausa. Ga kashi na hudu, kuma na karshen hirar.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Yanzu akwai sojoji da yawa irinka da suka watsar da aikin soja saboda bacin ransu irin naka?

Soja: Wallahi Tallahi sojojin ma da suka bullo ta daji, wadanda an gudu an barsu a daji, da suke bullowa wasu da yawa, suna ajje bindigarsu suna wucewa gidajensu, fiye da mutum ishirin. Fiye da mutum ishirin nace maka yanzu haka a wannan bataliyar da muke a Kwanduga. Ko ni da nake maka maganar nan yanzu, yanzu haka ina shirin wucewa ne kawai, kawai ina kokarin fada wa duniya ne, ta san abunda ke faruwa. Wadannan mutanen a asirance suke yin abun, da saninsu komai.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Baka tsoron abunda rundunar sojan zata yi, tazo tana nemanku bayan kun tafi?

Soja: Wallahi yanzu haka yara suna nan a daji ma mun fito ma. Ana ta cewa wai ana ta tura sojoji , tura sojoji, karya ne. Duk sojojin da suke Maiduguri ana cewa sun fi dubu goma, karya ne. In muna da sojoji dubu goma anan, da Boko Haram sun kare. Boko Haram din su nawa ne?

Aliyu Mustaphan Sokoto: Sojojin nawa ne?

Soja: Duka sojojin da muke nan, in an hada lissafi… kuma an kar kasa su, domin garin ba karamin gari bane. Maiduguri babban gari ne. To mu da muke cikin Kwanduga duka mu wajen dari da wani abu ne, kuma mu dinne kadai muke ja dasu. Don saboda mu babu munafukai a cikinmu, bamu jima ba. Duk wani sojan da ya……... ya riga ya zama dan Boko Haram, idan ba haka ba, she** nake. A cire su a kawo sojoji su zo suce zasu yi aikinnan, kwana daya, a shiga a je a yi “clearing” sama da kasa wannan abun ya kare. Amma bari in gaya maka idan basu yi haka ba, to walLahi gwamnatin nan da take zaluntar ‘yan arewa saboda a samu a ci musu galaba, kasan arewa itace take da karfi a Najeriya. Ana nema a nakasata ne, saboda kaga zabe ya iso, ayi “confusing” din mutane lokacin zabe ku zoma ku gagara sanin abunda akeyi har a gama abunda za’a yi. Ka saka wannan maganar nawa duka a radiyo, karka wani boyewa fa.

Aliyu Mustaphan Sokoto: To mun gode kwarai da gaske.

Soja: A taimaka, a raya “innocent soul”, ana ta kashe wadanda basu jiba, basu gani ba. Ana kashe mutane a nan wajen Oga, bazan boye maka ba. Ana kashe “innocent ones” oo, gara duniya ta sani. Kuma wallahi idan basu iya “controlling” wannan abun yanzu ba, har su mutu su kansu sai anzo an same su har gida. Idan kayi korafi, sai ka ga an yi maka oda, an yi “dismissing” dinka. Don Allah a saka wannan maganar duka. Najeriya Army da gwamnatin Najeriya su suke kashe mutanen Maiduguri oo.

Yanzu kusan kwanaki shida kennan Sashen Hausa yake neman hukumomin Najeriya, a ciki harda yawan kiran babban sakataren ma'aikatar tsaron Najeriya, Alhaji Aliyu Noma domin mu basu damar mayar da martani ga wadannan kalaman amma bamu samu ji daga wajensu ba.
XS
SM
MD
LG