Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’amuran Da Ke Tattare Da Zaben Jamhuriyar Nijar


Zaben Nijar

A ranar Lahadi 27 ga watan Disamba al’umar Nijar za ta yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki, inda hankulan mutane ya fi karkata kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, tsaro da kuma annobar coronavirus.

‘Yan takara Talatin ne ke neman kujerar shugaban kasa, amma kamar yadda wakilinmu Mahmud Lalo da ke birnin Yamai ya lura, akwai alamu da ke nuna rashin armashi tattare da zaben.

Babban birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ya sha kwalliya da manyan allunan hotunan ‘yan takarar shugaban kasa, wadanda tamkar suna kallon jama’ar da ke ta gitttawa ne, yayin da ake ta kamfe din zaben shugaban kasa da na kujerar ‘yan majalisar dokoki 171.

Sai dai a gefe guda, akwai alamu da ke nuna alamun babu armashi tattare da wannan zabe.

“Ba a taba zabe na dandatse ba, kowa tafiya yake bai san inda za a je ba, don haka dole mutane su yi dardar, wasu sun shirya wasu basu shirya ba.” In ji Alhaji Nasirou Saidou na Kungiyar Muryar Talaka, mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum.

Kotun Tsarin mulki, ta soke takarar Hama Amadou na jam’iyyar Moden Lumana, wanda tsohon kakakin majalisar dokoki ne, wanda har ila yau ya taba rike mukamin firai Ministan har sau biyu, bisa wasu dalilai da suka shafi badakalar safarar jarirai da aka same shi da laifi a shekarar 2017.

Amma duk da haka, jami’iyyar ta ce za ta goyawa wani dan takara baya – inda a ranar Litinin da ta gabata ta zabi tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane na jam’iyyar RDR Canji a mastayin wanda za ta marawa baya.

“Soke takarar Hama Amadou da kotu ta yi hakan bayana nufin ba ruwanmu da zabe ba ne, abin da muka sa a gaba shi ne sauyi, kuma sauyin da Hama Amadou ko kuma da wanidan takara na gungun ‘yan adawa.” In ji Bana Ibrahim, jami’i a jam’iyyar Moden Lumana da ke adawa.

Bazoum Mohamed, wanda na hannun daman shugaba Mahamadou Issouhou mai barin gado ne, tsohon ministan harkokin wajen ne a jamhuriyar ta Nijar, shi ne kuma dan takarar PNDS Tarayya mai mulki.

Kuma ta yi wu, ya ci karensa ba babbaka saboda rashin kwakkwaran dan takara daga bangaren ‘yan adawa.

“Abin da ya sa muka ce muna tsammanin za mu lashe zabe tsakanin da Allah, idan aka hada jam’iyyun da ke goya Bazoum baya, wajen su 50 ne, sun ma wuce, kenan za mu samu abin da yahaura kashi 60 a cewar Tahirou Garka, jami’i a jam’iyya mai mulki ta PNDS.

Sai dai takarar ta Bazoum ta gamu da cikas, domin wasu daga cikin abokanan adawarsa, ciki har da Hama Amadou da aka soke takararsa, na ikrarin takardun shaidar zama dan kasa da Bazouma ya mallaka, na bogi ne.

A cewar Hama Amadou, “takardun naku na karya, ikon naku na karya ne. don haka don Allah mutanen Nijar, ku tashi tsaye, ba a ce ku fito ku yi fada ba, an ce ku fito ku yi zabe.

Nijar dai na da al’umar da yawanta ya haura miliyan 22, inda mutum miliyan bakwai da digo hudu ne suka yi rijistar zaben da ke tafe.

Da yawa dai daga cikin wadanda za su kada kuri’a irinsu Alhaji Salissou Amadou,sun ce burinsu shi ne, su samu shugaba na gari, wanda zai fitar da kasar daga kangin matsalar tsaro, komadar tattalin arziki da kuma coronavirus.

Muna fatan Allah ya ba mu shugaba tsarkakakke ingantacce wanda zai kawo kwanciyar hankali da tattalin arziki wanda zai zamanto idan an zabe shi hankalin al’umar Nijar zai kwanta gaba daya.”

Jamhuriyar Nijar, wacce ba ta da iyaka da ruwa, kan kasance hanya da masu zuwa cirani ke bi don kai wa ga nahiyar turai.

A yau kasar na fuskantar matsalolin da suka shafi fari, hare-haren ta’addanci da kuma rashin walwalar tattalin arziki.

Jama’a da dama dai za su zira ido ga duk dan takarar da ya lashe wannan zaben, domin ganin yadda zai kai kasar ga gaci.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Lalo:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00


Karin bayani akan Jamhuriyar Nijar, PNDS, da Hama Amadou.

XS
SM
MD
LG