Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al Shebab Ta Kashe Mutane Hudu a Gidan Cin Abinci


Wani yanki da kungiyar Al Shebab ta kai hari a Somalia
Wani yanki da kungiyar Al Shebab ta kai hari a Somalia

Kungiyar Al shebab ta maida hankalinta wajen kai hare-hare a wuraren cin abinci inda sukan kashe mutane da dama. A wani hari na baya-bayan nan da ta kai a wani gidan cin abinci, kungiyar ta kashe mutane hudu.

A Somalia, akalla fararen hula hudu ne suka rasa rayukansu kana wasu uku suka jikkata, bayan da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam din da ke jikinsa, a wani dan karamin gidan cin abinci a garin Baidoa.

Wadanda suka shaida harin sun fadawa Muryar Amurka cewa, maharin akan keke ya isa wurin, inda ya shiga gidan cin abincin da ake kira Barwaqo, ya ta da rigar bam din da ke jikinsa da farkon yammacin jiya Juma’a.

Rahotannin sun ce nan take mutane hudun suka mutu yayin da aka garzaya da wasu uku zuwa asibti.

Wakilin Muryar Amurka, a yankin na Baidoa, Muktar Mohammed Atosh, ya ce akwai mutane da dama da suka samu raunuka, amma da yawansu da kafarsu suka taka suka fice daga wurin.

Wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ta ce daga cikin wadanda suka mutu har da wani mai ayyukan jin-kai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG