Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Sun Fara Yajin Aiki a Najeriya


Asibitin koyarwa na Lagos

Yajin aikin 'yan kungiyar likitocin masu neman kwarewa a Najeriya ya kara jefa miliyoyin marasa lafiya cikin halin kaka na kayi a kasar.

Wannan yajin aikin ya shafi dukan asibitoci da cibiyoyin kula da kiwon lafiyar al’uma na gwamnatin tarayya da na jihohi wadanda likitoci masu neman kwarewa ke aiki a cikin su.

Matakin dai ya biyo cikar wa’adin da kungiyar likitocin ta baiwa gwamnatin tarayya ne na ta biya bukatun ‘ya ‘yanta wadanda suka hada da wadatattun kayan kariya daga cutuka masu saurin yaduwa irin Coronavirus da batun samar da kudaden bincike da nazari.

Dr Abubakar Nagoma Usman, shugaban reshen asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya bayyana damuwa a kan rashin dora ma’aikatan kiwon lafiya a kan inshoran lafiya duk da hadarin dake tattare da aikin suna yaki da cukuta masu yaduwa kamar Ebola da Lassa da kuma Coronavirus.

Sai dai shugabar sashin hulda da Jama’a na Asibitin koyarwa na Aminu Kanon, Hajiya Hawa Abdullahi ta ce hukumar asibitin ta cimma wata matsaya da kungiyar domin rage radadin yajin aikin akan marasa lafiya.

Sai dai duk da cewa, kwararrun likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya na ci gaba da aiki kamar yadda aka saba, akwai yuwuwar wannan yajin aiki ya yi mummunan tasiri akan tsarin kiwon lafiyar ‘yan najeriya, la’akari da cewa, adadin wadanda ke yajin aikin ya kai kimanin kashi 60% cikin dari.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG