Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS: Al-Baghdadi Ya Soki Saudiyya a Sabon Faifan Muryar Da Suka Saki


Wani Dan ISIS Dauke Da Tutarsu

Kungiyar ISIS sun fitar da wata sanarwa yau Asabar cewa, boyayyen shugabansu yana na kalua kuma suna ci gaba da dabarun yakinsu na salon daular Islama, sannan hare haren Rasha da wanda Amurka ma ke jagoranta na taron dangi ya kasa karya lagonsu.

Shugaban ya bayyan cewa Allah zai bamu nasara akan wadanda ba Allah suke bautawa ba. Sannan y ace yanayin zafin yaki yanayin tsarkinsa kenan a wajensu.

Jawabin na sautin muryar mai tsawon mintuna 24, ya bayyana sunan wanda yayi jawabin da suna Abu Bakr al-Baghdadi. Sakon ya soki kasar Saudiyya da kakkausar murya a yunkurinta na kafa sojojin taron dangin kasashen musulmi.

Inda al-Baghdadi ya yi kira ga ‘yan kasar Saudi da su tashi su yaki azzaluman Sarakunansu da suka hanasu katabus. Musamman ma yadda yace suna hada kai da yahudawa da sauran Turawan yamma ana yakarsu da sunan ta’addanci.

Sakon yazo daidai lokacin da ake dada samun rahoton rundunar sojin Iraki na dada kutsawa garin Ramadi a kokarin kwato garin daga hannun yan kungiyar ta Daish.

XS
SM
MD
LG