Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhamdulillahi Ina Samun Sauki – Maryam Yahaya 


Maryam Yahaya bayan da ta fara samun sauki (Instagram/Maryam Yahaya)
Maryam Yahaya bayan da ta fara samun sauki (Instagram/Maryam Yahaya)

An dai yi ta yamadidin cewa jifan ta aka yi, amma jarumar ta bayyana akasin hakan.

Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Yahaya, ta ce tana samun sauki bayan wani tsawon lokacin da ta kwashe tana fama da jinya.

“Alhamdulillahi, Alhamudulillahi, Alhamdulillahi. Allah na gode maka. Allah yana ba ni lafiya, ina godiya Allah Alhadulillahi. Jarumar ta Mansoor ta wallafa a shafinta na Instagram hade da wani hoton bidiyo da ya nunata sanye da hijabi mai ruwan rawaya.

An kwashe tsawon lokaci ba a jin duriyar Maryam wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu Tsakaninmu, Makota, Jaruma da Mujadala, lamarin da har ya kai ga ba ta wallafa hotuna a shafinta na Instagram kamar yadda ta saba.

A wata hira da ta yi da BBC Hausa, jarumar wacce ta fito idon duniya da fim din Mansoor, wanda ta yi tare da Umar M. Shariff, ta ce cutar typhoid da malaria ce ke damun ta.

An dai yi ta yamadidin cewa jifan ta aka yi, amma jarumar ta bayyana akasin hakan.

Gabanin hakan, an ga jarumai maza da mata a dandalin shirya fina-finan na Kannywood suna mata fatan samun sauki, abin da ya kara jaddada cewa tana kwance na rashin koshin lafiya.

Bayanai sun yi nuni da cewa abokanan sana’arta maza da mata, furodsoshi da darektoci sun yi ta tururuwar zuwa duba halin da take ciki tare da tallafa mata.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG