Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Najeriya Shehu Abdullahi Ya Auri Jarumar Kannywood


Shehu Abdullahi da amaryar Naja'atu (Instagram/Shehu Abdullahi)

Naja’atu ta fara fitowa a finan-finan Kannywood tun tana ‘yar matashiya inda daga baya ta zama daya daga cikin fitattun jarumai mata.

Dan wasan kwallon kafar Najeriya Shehu Abdullahi ya angwance tare da amaryarsa Naja’atu Muhammad Suleiman, wacce aka fi sani da Murjanatu ‘Yar Baba a fagen shirya fina-finan Kannywood.

An daura auren ne a birnin Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan sallar Juma’a.

Auren ya samu halartar 'yan uwa da abokanai ciki har da kyaftin Super Eagles Ahmed Musa.

Ango Shehu Abdullahi, (hagu) Ahmed Musa (dama) (Instagram/Shehu Abduallhi)
Ango Shehu Abdullahi, (hagu) Ahmed Musa (dama) (Instagram/Shehu Abduallhi)

Dan shekara 28, Shehu wanda dan wasan tsakiya ne, na buga kwallonsa a kungiyar Omonia ta kasar Cyrprus.

Naja’atu ta fara fitowa a finan-finan Kannywood tun tana ‘yar matashiya inda daga baya ta zama daya daga cikin fitattun jarumai mata.

Jama'a da dama ciki har da jaruman Kannywood da Nollywood, sun garzaya shafin Instagram din Shehu, inda ya wallafa hoton amaryarsa, suka taya sabbin ma'auratan murna.

"Allah ya sanya alheri." Yakubu Mohammed ya ce.

"Ina taya ku murna." Ali Nuhu ya rubuta, kamar yadda shi ma Ali Jita ya ce, "ina taya ku murna."

"Amaryarmu," In ji tsohuwar jaruma Mansura Isah.

"Ina taya ka murna Shehu, Allah ya ba ku zaman lafiya." In ji Aminu S. Bono, jarumi a Kannywood.

"Kykkyawa da ita." In ji Tonto Dikeh, jaruma a Nollywood.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG