Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhazan Najeriya Bakwai Ne Suka Rasu a Saudiyya Bana


Saudiyya

Gabanin hawan arfa da aka kammala Alhazan Najeriya bakwai ne suka rasa rayukansu yawancinsu don tsanantar hawan jini.

Shugaban kwamitin likitoci na hukumar alhazan Najeriya Dakta Ibrahim Kana, ya ce gabanin hawan arfa da aka kammala alhazan Najeriya bakwai ne suka rasu domin ciwon hawan jini.

Likatan ya bukaci alhazai su gujewa yawo a rana da su kuma rika shan ruwa, haka kuma ya bada tabbacin tanadar wadatattun magunguna ga alhazan har lokacin komawarsu gida.

Tun farko shugaban hukumar alhazan Barista Abdullahi Mohammad, ya jagoranci kwamitin malamai wajen addu’a ga dorewar zaman lafiya ga Najeriya da kara samun lafiya ga shugaba Mohammadu Buhari don samun damar aiwatar da muradun gwamnatinsa.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG