Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ALHERI GRACE ABDU: DOMIN IYALI: An Yiwa 'Yar Shekaru Biyu Fyade A Jihar Zamfara - Kashi Na Hudu, Mayu, 07, 2020


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A shirin Domin Iyali na wannan makon, wakilinmu Lamido Abubakar ya yi hira da wakilan kungiyar kare hakkokin mata da kananan yara WRAPA a jihar Zamfara, Zainab Nuhu jami’ar gudanarwa, da kuma Dahiru Mohammed jami’in ayyuka na kungiyar, dangane da batun zargin da wadansu iyaye suka yi a Kaurar Namoda cewa, wani dan shekaru talatin da ya bata karamar ‘yarsu ‘yar shekaru biyu.

A cikin hirarshi da Shirin Domin Iyali, Kakakin Rudunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara SP Shehu Mohammad ya tabbatar da cewa, 'yan sanda sun kai karamar yarinyar asibiti bayan samun rahoton yi mata fyade, kuma gwajin da aka gudanar ya tabbatar da cewa, babu shakka an yi mata fyade. Ya kuma ce sun kama wanda ake zargin mai suna Kabiru Nasiru.

Ga bayanin da jami'an kungiyar WRAPA na jihar Zamfara su ka yi wa shirin Domin Iyali

An Yiwa ,yar shekaru biyu fyade A Zamfara: Pt4-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:27 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG