WASHINGTON, DC —
Kakakin rundunar 'yan sandan jiharr Zamfara S.P. Shehu Mohammed , ya tabbatar da cewa,an yi wa karamar yarinya 'yar kasa da shekaru uku fyade kamar yadda iyayenta suka bayyana wa shirin Domin Iyali, sai dai yace sun kama mutumin kuma har i zuwa lokacin da shirin ya yi hira da shi, mutumin yana kulle ana jira a gurfanar da shi a kotu,
Kakarin rundunar 'yan sandan ya kuma ce sun kai karamar yarinyar asibiti inda likitoci suka gwada ta suka kuma tabatar da cewa an yi mata fyade.
Saurari bayanin da ya yi a hirar shi da wakilin Sashen Hausa Lamido Abubakar.
Facebook Forum