Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkawuran Wasu 'Yan Takarar Gwamna Karkashin Jam'iyyu Daban-daban A Najeriya


Wadansu 'yan takarar gwamna tare da Aliyu Mustapha Sokoto
Wadansu 'yan takarar gwamna tare da Aliyu Mustapha Sokoto

Wasu masu neman takarar kujerar gwamna a jihohin Najeriya na ci gaba da yin alkawura idan jama'a suka ba su dama a zaben 2023.

A daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke dada shiga wani irin yanayi a game da zaben shugabanni adalai a matakai da suka hada da ‘yan majalisu, gwamnoni, da ma shugaba da zai jagoranci kasar a zaben shekarar 2023 mai gabatowa.

‘Yan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyu kamar su APC, PDP, SDP, NNPP da ma PRP na kara jadada mahimmancin samar da tsaro a cikin kudurorin da suka saka a gaba tun yanzu kafin su daura damarar aiki idan Allah ya basu nasara a zaben shekarar 2023 a jihohinsu da suke neman takara.

Jihohin arewacin Najeriya musamman arewa maso yamma kamar su Kaduna, Katsina, Zamfara, Kebbi,Sakkwato da arewa maso tsakiya kamar su Neja, Nasarawa, arewa maso gabas: Yobe, Borno, Bauchi da dai sauransu na fama da matsalolin tsaro, koma baya a fannin ilimi, tattalin arziki da kudaden shiga, talauci, yawan yaran da ba sa makaranta da dai sauransu.

Wadannan matsalolin dai ya sanya masu fafutukar ganin an zabi shugabanni da ke da kwarewa da ma sanin makamar aiki bayyana mahimmancin duba cancanta da zabar masu kishin al’umma a zaben shekarar 2023 a duk matakan gwamnati.

Ga manya da kananan jam’iyyun siyasar kasar nan, tambayar da al’umma ke yiwa masu neman kujerar gwamna shi ne mene ne zasu yi na daban idan aka zabe su.

Dan takarar gwamna a jihar Bauchi karkashin inuwar jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, Sanata Halliru Jika, ya ce ya shirya tsaf inda ya kawo kwararru suka fitar masa da tsare-tsare ta yadda za su sa rayuwar al’amura jihar Bauchi ta yi sauki.

Wa’adin Mako 6 Da Muka Baiwa Buhari Kadan Ne Daga Cikin Shirin Majalisa- Sanata Jika ​​​​​​
please wait

No media source currently available

0:00 0:14:56 0:00

A wani bangare kuma dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Hon. Muhammad Umaru Bago, ya fadi abubuwan da zai fara yi idan ya sami nasara a zaben shekarar 2023.

Abu na farko shi ne tsaro sannan harkokin noma saboda yadda Allah ya bai wa jihar girman fadin kasa.

Suma wasu ‘yan takara gwamna a jihohin Adamawa, Kano, Katsina sun bayyana kudurorinsu, da suka hada da yaki da talauci, yunwa, samar da aikin yi, ilimi, bunkasa kasuwanci da dai sauransu.

A na su bangaren wasu ‘yan kasar sun bayyana ra’ayoyinsu kan alkawuran da masu neman takarar gwamnan ke yi, suna cewa fatansu Allah ya sa su cika alkawuran da suka dauka.

A bisa jadawalin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, za’a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisun tarayyar a ranar 25 ga watan Febrairu na shekarar 2023, daga bisani a shiga babin na gwamnoni da 'yan majalisu a jihohin kasar 36 a ranar 11 ga watan Maris.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:41 0:00

XS
SM
MD
LG