Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah ya Kubutar da Wasu Mata Daga Hannun Boko Haram


Irin mata da yaran dake cikin tagayyara a sassa daban-dabn na arewa maso gabashin Najeriya sanadiyar hare-hare ko sace-sacen 'yan Boko Haram.

Daya daga cikin matan da suka kubuta ta ce 'yan Boko Haram ne ke rike da garuruwan su, babu soja ko daya

Allah Ya kubutar da wasu mata fiye da sittin da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a kauyukan kananan hukumomin Madagali da Michika.

Daya daga cikin matan nan da suka samu tserewa ta yi bayani a tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, amma ta bukaci ya rufa ma ta asiri, kar ya bayyanawa duniya sunan ta. Ga bayanin da ta yi game da yadda aka sace su, da kuma irin wahalar da ta sha a hanyar tserewa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

A cewar wannan mata da ta bayar da shaida, yanzu haka akwai sauran wasu matan su kusan arba'in a hannun 'yan kungiyar Boko Haram. Kuma ta ce babu wani soja a yankin su, saboda haka 'yan Boko Haram ne kawai ke cin karen su ba babbaka a garuruwan su.

XS
SM
MD
LG