Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya Yi Wa Matar Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa Rasuwa


Sir Abubakar Tafawa Balewa
Sir Abubakar Tafawa Balewa

Allah ya yi wa matar marigayi Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa, mai suna Hajiya Aishatu Balewa, rasuwa.

Wata sanarwa mai sauke da sa hannun babban Mataimaki na Musamman kan harkokin Yada Labarai na Gwamnan jahar Bauchi, Mukhtar Gidado na cewa, "Mai Girma gwamnan Bauchi Bala A. Mohammed ya tabbatar da rasuwar Hajiya Aishatu (Jummai) Balewa, matar marigayi Firayim Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Marigayiyar ta rasu A ranar Lahadi 27 ga Oktoba, 2019, a wani asibiti da ke birnin Legas, ta rasu ne tana da shekara 85 bayan wata dogowar rashin lafiya."

Sanarwar ta cigaba da cewa za’a yi Sallar jana'izar ta a yau dinnan Litini a fadar Sarkin Bauchi da karfe 2 na yamma.

Sanarwar ta kara da cewa, "Gwamnan Bauchi Bala Mohammed a madadin Gwamnati da mutanen jihar Bauchi tare da iyalan marigayi Firayim Minista ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ba wai kawai ga dangin ta na kusa ba, ya ce wannan rashi ne babban ga jama'ar jihar Bauchi da Najeriya baki daya"

Marigayiya Hajiya A'ishatu, wacce ake kuma kira Jummai, ta rasu ta bar 'ya'ya 8 da kuma jikoki masu yawa.

Ga wakilinmu a Bauchi Abdulwahab Muhammad da karin bayani a hira da Mahmud Lalo ya yi da shi ta waya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG