Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Rohingya Na Arcewa Daga Myanmar Sanadiyar Tarzoma Da Kutuntawa


Raad Al Hussein shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD

Shugaban hukumar dake kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ya fada a rahotonsa cewa al'ummar Rohingya na ci gaba da arcewa daga kasarsu saboda tarzoma da kutuntawa da ake yi masu

Shugaban hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Raad Al Hussein ya bada rahoton cewa dubban yan gudun hijira yan kabilar Rohingya suna ci gaba da arcewa tarzoma da kuntuta musu da ake yi a kasar Myanmar.

Yace hukumomi Myanmar suna kokarin su shawo kan duniya cewa a shirye suke, zasu bari yan gudun hijira su koma gidajensu. To amma Mr Zeid ya musunta wannan ikirari. Yace yana da shedar mutane kalilan da suka koma don radin kansu an garkama su a gidan yari kuma an musguna musu.

Yace dukkan yan gudun hijira da suka koma da ofishin hukumar sa ta zanta da su, sun baiyana yadda ake ci gaba da yi musu tarzoma da musguna musu da take yancin su, ciki harda karkashe wasu da kuma kona gidajen wasu yan kabilar Rohingya. Mutane suna ci gaba da arcewa kunci daga jihar Rakhine, harma wasu dake arcewa sun gwamace ko kuma a shirye suke sun fuskanci yiwuwar su mutu a teku, domin kawai su tsira daga musguna musu da ake yi.

A saboda haka Me Zeid ya bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya daya kai karar kasar Myanmar gaban kotun kasa da kasa, domin a bincike zarge zargen musugunawa da kuma kisan kiyashen da aka yiwa yan kabilar Rohingya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG