Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD: Bara An Kashe Yara Fiye da Dubu 10 An Ci Zarafin Dubu 21 a Duniya


Hukumar dake kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya

Alkalumman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar akan yara sun nuna yara fiye da dubu goma aka kashe ko aka nakasasu kana an ci zarafin wasu dubu ishirin da daya a duk fadin duniya sanadiyar tashe tashen hankali

Yara fiye da 10,000 ne aka kashe ko aka nakasa bara a tashe-tashen hankula a duk fadin duniya, a cewar wani rahoto na MDD.

An samu rahotannin mummunan cin zarafin yara har sau 21,000 a 2017, wanda ya nuna karuwar al'amarin sosai idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, a cewar sakamakon binciken sashin nazarin tashe-tashen hankula da makomar yara.

"Yara kanana - maza da mata - sun kadu sosai da tashe-tashen hankulan da aka dade ana yi da kuma sabbi. Duk kuwa da cigaban da aka dan samu, har yanzu irin cin zarafin yara da ake yi ba abin yadda ba ne," a cewar wani mai magana da yawun Sakatare-Janr na MDD Antonio Gueterres a wata takardar bayani.

Rahoton ya tabo kasashe 20, ciki har da wuraren da al'amarin ya fi tsanani kamar su Yemen, da Siriya da kuma Afghanistan.

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG