Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’umomin kasar Nijar Sun Nemi ‘Yan Najeriya Su Kaucewa Tashin Hankali


Zaben Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna Jamhuriyar Nijar
Zaben Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna Jamhuriyar Nijar

'Yan kasar Nijar sun yi kira ga al'umomin Najeriya da 'yan siyasa su kaucewa duk wasu hanyoyi da zasu haddasa tashin hankali a kasar lokacin zabe.

Al’umomin jamhuriyar Nijar na ci gaba da kiraye-kiraye ga 'yan siyasa da ma al'umar Najeriya baki daya don kaucewa dukkan wata tarzomar dake da nasaba da rikicin zabe tare da jan hankulan 'yan Nijar mazauna Najeriyar su nisanci kansu da shiga dukkan wata harkar da ta shafi zaben na Najeriya.

Lura da zazzafan kalaman wasu daga cikin 'yan siyasar ta Najeriya a yayin yakin zaben da aka kammala a jiya Alhamis ya sa 'yan Nijar jan hankulan bangarorin siyasa akan bukatar su yi karatun ta nutsu don ganin komai na wannan zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Saboda haka nuna halin dattako ya zama wajibi ga kowane dan Najeriya, Hajiya Zara Maina, wata tsohuwar 'yar jarida ce dake bin diddigin harakokin siyasar Najeriya. Ta ce samun tashin hakali a Najeriya ya shafi mutanen Nijar.

Kamar yadda doka ta haramtawa kowane mutun tsoma hannunsa a harakokin siyasar kasar da ba ta shi ba, ya sa wani mai sharhi akan al'amuran yau da kullum Ibrahim Amadou, tunatar da 'yan Nijar mazauna Najeriya nauyin da ya rataya a wuyansu game da zaben na 16 ga watan Fabareru.

A yadda wannan zabe ke daukan hankalin jama'ar Nijar Shuwagabanin addinai sun dukufa ga addu’oin zaman lafiya tare da gargadin matasa su nisanci duk wani dan siyasar da zai yunkura amfani da su don tayar da bore akan maganar zabe.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG