Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliya Ta Jefa Al'ummar Somalia Cikin Halin Kakanikayi


Ambaliya a Somalia
Ambaliya a Somalia

Yawan ruwan ambaliya a yankunan kudancin Somalia ya fidda sama da mutum dubu 650 daga gidajen su a cikin wannan shekara.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta ce ambaliyar tayi sanadiyar karancin abinci da ya kai ga barkewar cututtuka masu kisa kana ya kara fargabar karin yaduwar coronavirus a cikin kasar.

Sama mutum dubu dari da hamsin da ambaliyar ta rutsa dasu sun rasa mtsugunai a karshen watan Yuni, ciki har da mutum dubu 23 da suka rasa muhallan su a makon da ya gabatan nan, a cewar jami’ai. Masu hasashen yanayi sun ce har yanzu da sauran rina a kaba. Sun yi hasashen cewa akwai ruwa kamar da bakin kwarya da kuma ambaliya mai munin gaske da za a ci gaba da gani a wasu yankuna har izuwa wani lokaci kana zai addabi rayuwar dubun dubatar mutane kuma ya raba su da matsugunan su.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijiran ta MDD, Charlie Yaxley ya yita fadar cewa sababbin wadanda suka rasa matsugunan su, suna wani wurin mai yawan mutane, wasu matsugunai mara kariya dake fama da yanayi mara kyau. Ya ce iyalai na huskantar barazanar karuwan miyagun ayyuka kamar fashi da fyade.

Sai dai Yaxley ya ce ba a samu wani labarin barkewar coronavirus mai yawa ba amma ya fadawa Muryar Amurka lamarin ya yi muni. Ya ce mutane basu samun ruwa mai tsafta, cunkuso a sansani yana hana nesanta da juna kana babu isasshen ban-daki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG