Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliya Ta Kashe Mutane Da Dama A Afghanistan


Ambaliyar Ruwan Sama A Afghanistan
Ambaliyar Ruwan Sama A Afghanistan

Jami’an kasar Afghanistan sun fadi a ranar Lahadi cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya daga lokacin damuna a gabashin kasar, a wasu yankuna da ke makwabtaka da kasar Pakistan, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30 a cikin dare.

Wani hoton faifan bidiyo na kamfanin dillanci labaran Associated Press ya nuna kauyawa a gundumar Khushi da ke lardin Logar da ke kudu da birnin Kabul, babban kasar Afghanistan suna share-share bayan ambaliyar ruwan, inda gidaje suka lalace.

Shugaban hukumar yaki da bala’o’i na lardin, Abdullah Mufaker, ya ce har yanzu ba’a san adadin wadanda suka mutu da kuma jikkata ba sakamakon tashin ruwanba, amma akwai akalla mutane tara da suka mutu.

“Ba’a bayyana ainihin adadin ba, kuma mutane sun je sun kwashe gwarwakin,” in ji shi.

Del Agha, dattijon kauyen, ya ce ba’a taba ganin irinta wanan ambaliyar ruwan a tarihin Khushi. Ya ce ta lalata dukkan dabbobin mutane, gidaje da filayen noma. Mutane sun rasa matsugunansu, lamarin da ya tilasta musu neman mafaka a tsaunuka.

A makwabciyar kasar Pakistan, ambaliyar ruwan da mamakon ruwan saman ya haddasa, ta kashe mutane akalla 36, ciki har da 11 da suka mutu a yankunan da ke kan iyaka da kasar Afghanistan, a cewar hukumar kula da bala’o’i ta kasar.

Masu aikin ceto da sojoji ke marawa baya sun kwashe duban mutane da suka makale zuwa wani wurin, yayin da ake sa ran ruwan sama a wannan makon a Pakistan.

Lokacin damuna yana farawa ne daga watan Yuli zuwa Satumba.

A makon da ya gaba, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa da ta kashe akalla mutane 31 tare da bacewar wsu da dama a arewacin Afgahanistan.

XS
SM
MD
LG