Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyan Ruwa Ya Lalata Hanyoyi A Jihohi Takwas Na Jamhuriyar Nijar


Birnin Konni inda ma'aikatan sufuri da gine-gine na jihohi takwas din Nijar suka yi taronsu

Ma'aikatan ofishin ministocin sufuri da na gine-ginen hanyoyi na jihohi takwas a jamhuriyar Nijar ne suka taru a birnin Konni domin gudanar da tattaunawar kwanaki biyu akan lalacewar hanyoyinsu sanadiyar ambaliyan ruwa da canjin yanayi.

Malam Siraju Ibra ya bayyana dalilan da suka sa suka hade duk jihohin kasar guda takwas domin tattaunawar.

Inji Malam Ibra jamhuriyar Nijar na tsara yadda zata gina hanyoyinta to amma canjin yanayi yana shafar gine-ginensu dalili ke nan da suke son su duba lamarin da yadda zasu shawo kansa nan zuwa gaba.

Yace wani zibin sai a yi ruwa masu dimbin yawa da kan bata hanyoyi. Idan kuma an yi zafi fiye da kima ya kan lalata hanya. Iska ma tana yiwa hanyoyi illa. Suna duba duk wadannan domin idan za'a yi hanyoyin su san yadda za'a yisu su dore. Haka kuma za'a yi la'akari da karuwar motoci a kasar fiye da da can.

Shugaban ma'aikatar dake kula da gine-gine na jihar Agadez Malam Sha'aibu Adamu ya kara haske akan alfanun taron musamman a lokacin da kasashe kamar Nijar ke fuskantar canjin yanayi. Yace suna gini ga ruwa ga rana da zafi ga isaka ga kuma yawan dimbin kasa. Duk wadannan abubuwa ne da suke shafar gine-ginen da suka yi. Karatun da suka yi na gina hanya bai yi la'akari da wadannan abubuwa ba. Yanzu dole su sake lale a shirye-shiryensu.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

XS
SM
MD
LG