Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Da Ba'a Taba Ganin Irinta Ba Na Ci Gaba Da Hallaka Jama'a


Zuwa jiya Labara, Adadin mace-mace ya haura zuwa 11 a Baton Rouge, yayin da hedikwatar ta jahar Louisiana ke fama da wata irin ambaliyar ruwan da ba a taba gani ba.

Gidaje kimanin dubu 40 sun lalace, bayan da aka sheka ruwa mafi tsanani a tarihin Baron Rouge. Jami'an Hukumar Aikin Agajin Gaggawa ta (FEMA) da masu kai gudunmowa sun kasance a wurin na tsawon kwanaki, kamar yadda 'yan agajin Red Cross su ka yi.

"Daidai ne a ce wannan jaha ta saba da guguwa mai ambaliyar ruwa," a cewar Craig Cooper na hukumar Red Cross ga Muryar Amurka, wanda ya kara da cewa, "to amma wannan wani irin ruwan sama ne innanaha, kuma abin da mu ka ji shi ne a sassa da dama, al'ummomi ba su taba ganin ambaliyar ruwa ba, ko kuma rabon su ga ambaliya irin wannan tun shekaru 30 da su ka gabata."

Cooper ya yi gargadin cewa har yanzu al'amarin na Baton Rouge Rouge na cigaba da daukar sabon salo, a yayin aka cigaba da ayyana wurare yankunan da ke karkashin dokar ta baci, ana ganin karin baran da kuma karuwar mace-mace.

An ceto mutane 30,000 tun daga ranar Jumma'a.

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG